نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5987 | 88 | 20 | وإلى الأرض كيف سطحت |
| | | Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? |
|
5988 | 88 | 21 | فذكر إنما أنت مذكر |
| | | sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. |
|
5989 | 88 | 22 | لست عليهم بمصيطر |
| | | Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. |
|
5990 | 88 | 23 | إلا من تولى وكفر |
| | | Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. |
|
5991 | 88 | 24 | فيعذبه الله العذاب الأكبر |
| | | To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. |
|
5992 | 88 | 25 | إن إلينا إيابهم |
| | | Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. |
|
5993 | 88 | 26 | ثم إن علينا حسابهم |
| | | Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. |
|
5994 | 89 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والفجر |
| | | Inã rantsuwa da alfijiri. |
|
5995 | 89 | 2 | وليال عشر |
| | | Da darũruwa gõma. |
|
5996 | 89 | 3 | والشفع والوتر |
| | | Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. |
|