نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5983 | 88 | 16 | وزرابي مبثوثة |
| | | Da katifu shimfiɗe. |
|
5984 | 88 | 17 | أفلا ينظرون إلى الإبل كيف خلقت |
| | | Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? |
|
5985 | 88 | 18 | وإلى السماء كيف رفعت |
| | | Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? |
|
5986 | 88 | 19 | وإلى الجبال كيف نصبت |
| | | Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? |
|
5987 | 88 | 20 | وإلى الأرض كيف سطحت |
| | | Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? |
|
5988 | 88 | 21 | فذكر إنما أنت مذكر |
| | | sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. |
|
5989 | 88 | 22 | لست عليهم بمصيطر |
| | | Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. |
|
5990 | 88 | 23 | إلا من تولى وكفر |
| | | Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. |
|
5991 | 88 | 24 | فيعذبه الله العذاب الأكبر |
| | | To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. |
|
5992 | 88 | 25 | إن إلينا إيابهم |
| | | Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. |
|