نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5970 | 88 | 3 | عاملة ناصبة |
| | | Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. |
|
5971 | 88 | 4 | تصلى نارا حامية |
| | | Zã su shiga wata wuta mai zãfi. |
|
5972 | 88 | 5 | تسقى من عين آنية |
| | | Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. |
|
5973 | 88 | 6 | ليس لهم طعام إلا من ضريع |
| | | Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. |
|
5974 | 88 | 7 | لا يسمن ولا يغني من جوع |
| | | Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. |
|
5975 | 88 | 8 | وجوه يومئذ ناعمة |
| | | Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. |
|
5976 | 88 | 9 | لسعيها راضية |
| | | Game da aikinsu, masu yarda ne. |
|
5977 | 88 | 10 | في جنة عالية |
| | | (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. |
|
5978 | 88 | 11 | لا تسمع فيها لاغية |
| | | Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. |
|
5979 | 88 | 12 | فيها عين جارية |
| | | A cikinta akwai marmaro mai gudãna. |
|