نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5949 | 87 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم سبح اسم ربك الأعلى |
| | | Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. |
|
5950 | 87 | 2 | الذي خلق فسوى |
| | | Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. |
|
5951 | 87 | 3 | والذي قدر فهدى |
| | | Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). |
|
5952 | 87 | 4 | والذي أخرج المرعى |
| | | Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. |
|
5953 | 87 | 5 | فجعله غثاء أحوى |
| | | Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. |
|
5954 | 87 | 6 | سنقرئك فلا تنسى |
| | | Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. |
|
5955 | 87 | 7 | إلا ما شاء الله إنه يعلم الجهر وما يخفى |
| | | Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. |
|
5956 | 87 | 8 | ونيسرك لليسرى |
| | | Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. |
|
5957 | 87 | 9 | فذكر إن نفعت الذكرى |
| | | Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. |
|
5958 | 87 | 10 | سيذكر من يخشى |
| | | Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. |
|