نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5917 | 85 | 8 | وما نقموا منهم إلا أن يؤمنوا بالله العزيز الحميد |
| | | Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. |
|
5918 | 85 | 9 | الذي له ملك السماوات والأرض والله على كل شيء شهيد |
| | | Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. |
|
5919 | 85 | 10 | إن الذين فتنوا المؤمنين والمؤمنات ثم لم يتوبوا فلهم عذاب جهنم ولهم عذاب الحريق |
| | | Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. |
|
5920 | 85 | 11 | إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات لهم جنات تجري من تحتها الأنهار ذلك الفوز الكبير |
| | | Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. |
|
5921 | 85 | 12 | إن بطش ربك لشديد |
| | | Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. |
|
5922 | 85 | 13 | إنه هو يبدئ ويعيد |
| | | Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). |
|
5923 | 85 | 14 | وهو الغفور الودود |
| | | Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. |
|
5924 | 85 | 15 | ذو العرش المجيد |
| | | Mai Al'arshi mai girma |
|
5925 | 85 | 16 | فعال لما يريد |
| | | Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. |
|
5926 | 85 | 17 | هل أتاك حديث الجنود |
| | | Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. |
|