نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5912 | 85 | 3 | وشاهد ومشهود |
| | | Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa |
|
5913 | 85 | 4 | قتل أصحاب الأخدود |
| | | An la'ani mutãnen rãmi. |
|
5914 | 85 | 5 | النار ذات الوقود |
| | | Wato wuta wadda aka hura. |
|
5915 | 85 | 6 | إذ هم عليها قعود |
| | | A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. |
|
5916 | 85 | 7 | وهم على ما يفعلون بالمؤمنين شهود |
| | | Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. |
|
5917 | 85 | 8 | وما نقموا منهم إلا أن يؤمنوا بالله العزيز الحميد |
| | | Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. |
|
5918 | 85 | 9 | الذي له ملك السماوات والأرض والله على كل شيء شهيد |
| | | Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. |
|
5919 | 85 | 10 | إن الذين فتنوا المؤمنين والمؤمنات ثم لم يتوبوا فلهم عذاب جهنم ولهم عذاب الحريق |
| | | Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. |
|
5920 | 85 | 11 | إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات لهم جنات تجري من تحتها الأنهار ذلك الفوز الكبير |
| | | Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. |
|
5921 | 85 | 12 | إن بطش ربك لشديد |
| | | Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. |
|