نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5885 | 84 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم إذا السماء انشقت |
| | | Idan sama ta kẽce, |
|
5886 | 84 | 2 | وأذنت لربها وحقت |
| | | Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, |
|
5887 | 84 | 3 | وإذا الأرض مدت |
| | | Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, |
|
5888 | 84 | 4 | وألقت ما فيها وتخلت |
| | | Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. |
|
5889 | 84 | 5 | وأذنت لربها وحقت |
| | | Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, |
|
5890 | 84 | 6 | يا أيها الإنسان إنك كادح إلى ربك كدحا فملاقيه |
| | | Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. |
|
5891 | 84 | 7 | فأما من أوتي كتابه بيمينه |
| | | To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. |
|
5892 | 84 | 8 | فسوف يحاسب حسابا يسيرا |
| | | To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. |
|
5893 | 84 | 9 | وينقلب إلى أهله مسرورا |
| | | Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. |
|
5894 | 84 | 10 | وأما من أوتي كتابه وراء ظهره |
| | | Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. |
|