نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5876 | 83 | 28 | عينا يشرب بها المقربون |
| | | (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. |
|
5877 | 83 | 29 | إن الذين أجرموا كانوا من الذين آمنوا يضحكون |
| | | Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. |
|
5878 | 83 | 30 | وإذا مروا بهم يتغامزون |
| | | Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. |
|
5879 | 83 | 31 | وإذا انقلبوا إلى أهلهم انقلبوا فكهين |
| | | Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci. |
|
5880 | 83 | 32 | وإذا رأوهم قالوا إن هؤلاء لضالون |
| | | Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne." |
|
5881 | 83 | 33 | وما أرسلوا عليهم حافظين |
| | | Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu. |
|
5882 | 83 | 34 | فاليوم الذين آمنوا من الكفار يضحكون |
| | | To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya. |
|
5883 | 83 | 35 | على الأرائك ينظرون |
| | | A kan karagu, suna ta kallo. |
|
5884 | 83 | 36 | هل ثوب الكفار ما كانوا يفعلون |
| | | Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa? |
|
5885 | 84 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم إذا السماء انشقت |
| | | Idan sama ta kẽce, |
|