نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5869 | 83 | 21 | يشهده المقربون |
| | | Muƙarrabai suke halarta shi. |
|
5870 | 83 | 22 | إن الأبرار لفي نعيم |
| | | Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima. |
|
5871 | 83 | 23 | على الأرائك ينظرون |
| | | A kan karagu, suna ta kallo. |
|
5872 | 83 | 24 | تعرف في وجوههم نضرة النعيم |
| | | Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima. |
|
5873 | 83 | 25 | يسقون من رحيق مختوم |
| | | Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta. |
|
5874 | 83 | 26 | ختامه مسك وفي ذلك فليتنافس المتنافسون |
| | | ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma. |
|
5875 | 83 | 27 | ومزاجه من تسنيم |
| | | Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake. |
|
5876 | 83 | 28 | عينا يشرب بها المقربون |
| | | (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. |
|
5877 | 83 | 29 | إن الذين أجرموا كانوا من الذين آمنوا يضحكون |
| | | Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. |
|
5878 | 83 | 30 | وإذا مروا بهم يتغامزون |
| | | Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. |
|