نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5858 | 83 | 10 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. |
|
5859 | 83 | 11 | الذين يكذبون بيوم الدين |
| | | Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako. |
|
5860 | 83 | 12 | وما يكذب به إلا كل معتد أثيم |
| | | Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi. |
|
5861 | 83 | 13 | إذا تتلى عليه آياتنا قال أساطير الأولين |
| | | Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne. |
|
5862 | 83 | 14 | كلا بل ران على قلوبهم ما كانوا يكسبون |
| | | A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu. |
|
5863 | 83 | 15 | كلا إنهم عن ربهم يومئذ لمحجوبون |
| | | A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne. |
|
5864 | 83 | 16 | ثم إنهم لصالو الجحيم |
| | | Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne. |
|
5865 | 83 | 17 | ثم يقال هذا الذي كنتم به تكذبون |
| | | Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi." |
|
5866 | 83 | 18 | كلا إن كتاب الأبرار لفي عليين |
| | | A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna? |
|
5867 | 83 | 19 | وما أدراك ما عليون |
| | | Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna? |
|