نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5846 | 82 | 17 | وما أدراك ما يوم الدين |
| | | Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako? |
|
5847 | 82 | 18 | ثم ما أدراك ما يوم الدين |
| | | Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako? |
|
5848 | 82 | 19 | يوم لا تملك نفس لنفس شيئا والأمر يومئذ لله |
| | | Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. |
|
5849 | 83 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم ويل للمطففين |
| | | Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa. |
|
5850 | 83 | 2 | الذين إذا اكتالوا على الناس يستوفون |
| | | Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu. |
|
5851 | 83 | 3 | وإذا كالوهم أو وزنوهم يخسرون |
| | | Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa |
|
5852 | 83 | 4 | ألا يظن أولئك أنهم مبعوثون |
| | | Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba? |
|
5853 | 83 | 5 | ليوم عظيم |
| | | Domin yini mai girma. |
|
5854 | 83 | 6 | يوم يقوم الناس لرب العالمين |
| | | Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta? |
|
5855 | 83 | 7 | كلا إن كتاب الفجار لفي سجين |
| | | Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn. |
|