نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5773 | 80 | 15 | بأيدي سفرة |
| | | A cikin hannãyen mala'iku marubũta. |
|
5774 | 80 | 16 | كرام بررة |
| | | Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. |
|
5775 | 80 | 17 | قتل الإنسان ما أكفره |
| | | An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! |
|
5776 | 80 | 18 | من أي شيء خلقه |
| | | Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? |
|
5777 | 80 | 19 | من نطفة خلقه فقدره |
| | | Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). |
|
5778 | 80 | 20 | ثم السبيل يسره |
| | | Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. |
|
5779 | 80 | 21 | ثم أماته فأقبره |
| | | Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. |
|
5780 | 80 | 22 | ثم إذا شاء أنشره |
| | | Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. |
|
5781 | 80 | 23 | كلا لما يقض ما أمره |
| | | Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). |
|
5782 | 80 | 24 | فلينظر الإنسان إلى طعامه |
| | | To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. |
|