نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5726 | 79 | 14 | فإذا هم بالساهرة |
| | | Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. |
|
5727 | 79 | 15 | هل أتاك حديث موسى |
| | | Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? |
|
5728 | 79 | 16 | إذ ناداه ربه بالواد المقدس طوى |
| | | A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? |
|
5729 | 79 | 17 | اذهب إلى فرعون إنه طغى |
| | | Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. |
|
5730 | 79 | 18 | فقل هل لك إلى أن تزكى |
| | | "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. |
|
5731 | 79 | 19 | وأهديك إلى ربك فتخشى |
| | | "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" |
|
5732 | 79 | 20 | فأراه الآية الكبرى |
| | | Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. |
|
5733 | 79 | 21 | فكذب وعصى |
| | | Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), |
|
5734 | 79 | 22 | ثم أدبر يسعى |
| | | Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. |
|
5735 | 79 | 23 | فحشر فنادى |
| | | Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. |
|