نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5717 | 79 | 5 | فالمدبرات أمرا |
| | | Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. |
|
5718 | 79 | 6 | يوم ترجف الراجفة |
| | | Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. |
|
5719 | 79 | 7 | تتبعها الرادفة |
| | | Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. |
|
5720 | 79 | 8 | قلوب يومئذ واجفة |
| | | Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. |
|
5721 | 79 | 9 | أبصارها خاشعة |
| | | Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. |
|
5722 | 79 | 10 | يقولون أإنا لمردودون في الحافرة |
| | | Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? |
|
5723 | 79 | 11 | أإذا كنا عظاما نخرة |
| | | "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" |
|
5724 | 79 | 12 | قالوا تلك إذا كرة خاسرة |
| | | Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" |
|
5725 | 79 | 13 | فإنما هي زجرة واحدة |
| | | To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. |
|
5726 | 79 | 14 | فإذا هم بالساهرة |
| | | Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. |
|