نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5702 | 78 | 30 | فذوقوا فلن نزيدكم إلا عذابا |
| | | Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba. |
|
5703 | 78 | 31 | إن للمتقين مفازا |
| | | Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo. |
|
5704 | 78 | 32 | حدائق وأعنابا |
| | | Lambuna da inabõbi. |
|
5705 | 78 | 33 | وكواعب أترابا |
| | | Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna. |
|
5706 | 78 | 34 | وكأسا دهاقا |
| | | Da hinjãlan giya cikakku. |
|
5707 | 78 | 35 | لا يسمعون فيها لغوا ولا كذابا |
| | | Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa. |
|
5708 | 78 | 36 | جزاء من ربك عطاء حسابا |
| | | Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa. |
|
5709 | 78 | 37 | رب السماوات والأرض وما بينهما الرحمن لا يملكون منه خطابا |
| | | Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi. |
|
5710 | 78 | 38 | يوم يقوم الروح والملائكة صفا لا يتكلمون إلا من أذن له الرحمن وقال صوابا |
| | | Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai. |
|
5711 | 78 | 39 | ذلك اليوم الحق فمن شاء اتخذ إلى ربه مآبا |
| | | Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa. |
|