نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5692 | 78 | 20 | وسيرت الجبال فكانت سرابا |
| | | Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. |
|
5693 | 78 | 21 | إن جهنم كانت مرصادا |
| | | Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. |
|
5694 | 78 | 22 | للطاغين مآبا |
| | | Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. |
|
5695 | 78 | 23 | لابثين فيها أحقابا |
| | | Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. |
|
5696 | 78 | 24 | لا يذوقون فيها بردا ولا شرابا |
| | | Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. |
|
5697 | 78 | 25 | إلا حميما وغساقا |
| | | Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini. |
|
5698 | 78 | 26 | جزاء وفاقا |
| | | Sakamako mai dãcẽwa. |
|
5699 | 78 | 27 | إنهم كانوا لا يرجون حسابا |
| | | Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi. |
|
5700 | 78 | 28 | وكذبوا بآياتنا كذابا |
| | | Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa! |
|
5701 | 78 | 29 | وكل شيء أحصيناه كتابا |
| | | Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce. |
|