نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5687 | 78 | 15 | لنخرج به حبا ونباتا |
| | | Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? |
|
5688 | 78 | 16 | وجنات ألفافا |
| | | Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? |
|
5689 | 78 | 17 | إن يوم الفصل كان ميقاتا |
| | | Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. |
|
5690 | 78 | 18 | يوم ينفخ في الصور فتأتون أفواجا |
| | | Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. |
|
5691 | 78 | 19 | وفتحت السماء فكانت أبوابا |
| | | Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. |
|
5692 | 78 | 20 | وسيرت الجبال فكانت سرابا |
| | | Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. |
|
5693 | 78 | 21 | إن جهنم كانت مرصادا |
| | | Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. |
|
5694 | 78 | 22 | للطاغين مآبا |
| | | Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. |
|
5695 | 78 | 23 | لابثين فيها أحقابا |
| | | Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. |
|
5696 | 78 | 24 | لا يذوقون فيها بردا ولا شرابا |
| | | Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. |
|