نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5682 | 78 | 10 | وجعلنا الليل لباسا |
| | | Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura? |
|
5683 | 78 | 11 | وجعلنا النهار معاشا |
| | | Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci? |
|
5684 | 78 | 12 | وبنينا فوقكم سبعا شدادا |
| | | Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi? |
|
5685 | 78 | 13 | وجعلنا سراجا وهاجا |
| | | Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)? |
|
5686 | 78 | 14 | وأنزلنا من المعصرات ماء ثجاجا |
| | | Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba? |
|
5687 | 78 | 15 | لنخرج به حبا ونباتا |
| | | Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? |
|
5688 | 78 | 16 | وجنات ألفافا |
| | | Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? |
|
5689 | 78 | 17 | إن يوم الفصل كان ميقاتا |
| | | Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. |
|
5690 | 78 | 18 | يوم ينفخ في الصور فتأتون أفواجا |
| | | Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. |
|
5691 | 78 | 19 | وفتحت السماء فكانت أبوابا |
| | | Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. |
|