نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5653 | 77 | 31 | لا ظليل ولا يغني من اللهب |
| | | Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta. |
|
5654 | 77 | 32 | إنها ترمي بشرر كالقصر |
| | | Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye. |
|
5655 | 77 | 33 | كأنه جمالت صفر |
| | | Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe. |
|
5656 | 77 | 34 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
|
5657 | 77 | 35 | هذا يوم لا ينطقون |
| | | Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba. |
|
5658 | 77 | 36 | ولا يؤذن لهم فيعتذرون |
| | | Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari. |
|
5659 | 77 | 37 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
|
5660 | 77 | 38 | هذا يوم الفصل جمعناكم والأولين |
| | | Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko. |
|
5661 | 77 | 39 | فإن كان لكم كيد فكيدون |
| | | To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita. |
|
5662 | 77 | 40 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
|