نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5641 | 77 | 19 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
|
5642 | 77 | 20 | ألم نخلقكم من ماء مهين |
| | | Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba. |
|
5643 | 77 | 21 | فجعلناه في قرار مكين |
| | | Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce. |
|
5644 | 77 | 22 | إلى قدر معلوم |
| | | Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna. |
|
5645 | 77 | 23 | فقدرنا فنعم القادرون |
| | | Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa. |
|
5646 | 77 | 24 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
|
5647 | 77 | 25 | ألم نجعل الأرض كفاتا |
| | | Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba. |
|
5648 | 77 | 26 | أحياء وأمواتا |
| | | Ga rãyayyu da matattu, |
|
5649 | 77 | 27 | وجعلنا فيها رواسي شامخات وأسقيناكم ماء فراتا |
| | | Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi? |
|
5650 | 77 | 28 | ويل يومئذ للمكذبين |
| | | Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
|