نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5619 | 76 | 28 | نحن خلقناهم وشددنا أسرهم وإذا شئنا بدلنا أمثالهم تبديلا |
| | | Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. |
|
5620 | 76 | 29 | إن هذه تذكرة فمن شاء اتخذ إلى ربه سبيلا |
| | | Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. |
|
5621 | 76 | 30 | وما تشاءون إلا أن يشاء الله إن الله كان عليما حكيما |
| | | Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. |
|
5622 | 76 | 31 | يدخل من يشاء في رحمته والظالمين أعد لهم عذابا أليما |
| | | Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. |
|
5623 | 77 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والمرسلات عرفا |
| | | Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. |
|
5624 | 77 | 2 | فالعاصفات عصفا |
| | | Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. |
|
5625 | 77 | 3 | والناشرات نشرا |
| | | Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. |
|
5626 | 77 | 4 | فالفارقات فرقا |
| | | sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. |
|
5627 | 77 | 5 | فالملقيات ذكرا |
| | | Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. |
|
5628 | 77 | 6 | عذرا أو نذرا |
| | | Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. |
|