نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5615 | 76 | 24 | فاصبر لحكم ربك ولا تطع منهم آثما أو كفورا |
| | | Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci. |
|
5616 | 76 | 25 | واذكر اسم ربك بكرة وأصيلا |
| | | Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice. |
|
5617 | 76 | 26 | ومن الليل فاسجد له وسبحه ليلا طويلا |
| | | Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo. |
|
5618 | 76 | 27 | إن هؤلاء يحبون العاجلة ويذرون وراءهم يوما ثقيلا |
| | | Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi. |
|
5619 | 76 | 28 | نحن خلقناهم وشددنا أسرهم وإذا شئنا بدلنا أمثالهم تبديلا |
| | | Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. |
|
5620 | 76 | 29 | إن هذه تذكرة فمن شاء اتخذ إلى ربه سبيلا |
| | | Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. |
|
5621 | 76 | 30 | وما تشاءون إلا أن يشاء الله إن الله كان عليما حكيما |
| | | Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. |
|
5622 | 76 | 31 | يدخل من يشاء في رحمته والظالمين أعد لهم عذابا أليما |
| | | Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. |
|
5623 | 77 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والمرسلات عرفا |
| | | Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. |
|
5624 | 77 | 2 | فالعاصفات عصفا |
| | | Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. |
|