نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5605 | 76 | 14 | ودانية عليهم ظلالها وذللت قطوفها تذليلا |
| | | Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. |
|
5606 | 76 | 15 | ويطاف عليهم بآنية من فضة وأكواب كانت قواريرا |
| | | Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. |
|
5607 | 76 | 16 | قوارير من فضة قدروها تقديرا |
| | | ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. |
|
5608 | 76 | 17 | ويسقون فيها كأسا كان مزاجها زنجبيلا |
| | | Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. |
|
5609 | 76 | 18 | عينا فيها تسمى سلسبيلا |
| | | Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. |
|
5610 | 76 | 19 | ويطوف عليهم ولدان مخلدون إذا رأيتهم حسبتهم لؤلؤا منثورا |
| | | Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. |
|
5611 | 76 | 20 | وإذا رأيت ثم رأيت نعيما وملكا كبيرا |
| | | Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba. |
|
5612 | 76 | 21 | عاليهم ثياب سندس خضر وإستبرق وحلوا أساور من فضة وسقاهم ربهم شرابا طهورا |
| | | Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki). |
|
5613 | 76 | 22 | إن هذا كان لكم جزاء وكان سعيكم مشكورا |
| | | (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa." |
|
5614 | 76 | 23 | إنا نحن نزلنا عليك القرآن تنزيلا |
| | | Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa. |
|