نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5601 | 76 | 10 | إنا نخاف من ربنا يوما عبوسا قمطريرا |
| | | "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." |
|
5602 | 76 | 11 | فوقاهم الله شر ذلك اليوم ولقاهم نضرة وسرورا |
| | | Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki, |
|
5603 | 76 | 12 | وجزاهم بما صبروا جنة وحريرا |
| | | Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini. |
|
5604 | 76 | 13 | متكئين فيها على الأرائك لا يرون فيها شمسا ولا زمهريرا |
| | | Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura. |
|
5605 | 76 | 14 | ودانية عليهم ظلالها وذللت قطوفها تذليلا |
| | | Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. |
|
5606 | 76 | 15 | ويطاف عليهم بآنية من فضة وأكواب كانت قواريرا |
| | | Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. |
|
5607 | 76 | 16 | قوارير من فضة قدروها تقديرا |
| | | ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. |
|
5608 | 76 | 17 | ويسقون فيها كأسا كان مزاجها زنجبيلا |
| | | Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. |
|
5609 | 76 | 18 | عينا فيها تسمى سلسبيلا |
| | | Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. |
|
5610 | 76 | 19 | ويطوف عليهم ولدان مخلدون إذا رأيتهم حسبتهم لؤلؤا منثورا |
| | | Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. |
|