نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5592 | 76 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم هل أتى على الإنسان حين من الدهر لم يكن شيئا مذكورا |
| | | Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. |
|
5593 | 76 | 2 | إنا خلقنا الإنسان من نطفة أمشاج نبتليه فجعلناه سميعا بصيرا |
| | | Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, |
|
5594 | 76 | 3 | إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا |
| | | Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. |
|
5595 | 76 | 4 | إنا أعتدنا للكافرين سلاسل وأغلالا وسعيرا |
| | | Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. |
|
5596 | 76 | 5 | إن الأبرار يشربون من كأس كان مزاجها كافورا |
| | | Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne. |
|
5597 | 76 | 6 | عينا يشرب بها عباد الله يفجرونها تفجيرا |
| | | Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. |
|
5598 | 76 | 7 | يوفون بالنذر ويخافون يوما كان شره مستطيرا |
| | | Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne. |
|
5599 | 76 | 8 | ويطعمون الطعام على حبه مسكينا ويتيما وأسيرا |
| | | Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme. |
|
5600 | 76 | 9 | إنما نطعمكم لوجه الله لا نريد منكم جزاء ولا شكورا |
| | | (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. |
|
5601 | 76 | 10 | إنا نخاف من ربنا يوما عبوسا قمطريرا |
| | | "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." |
|