نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5515 | 74 | 20 | ثم قتل كيف قدر |
| | | Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. |
|
5516 | 74 | 21 | ثم نظر |
| | | Sa'an nan, ya yi tunãni |
|
5517 | 74 | 22 | ثم عبس وبسر |
| | | Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. |
|
5518 | 74 | 23 | ثم أدبر واستكبر |
| | | Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, |
|
5519 | 74 | 24 | فقال إن هذا إلا سحر يؤثر |
| | | Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." |
|
5520 | 74 | 25 | إن هذا إلا قول البشر |
| | | "Wannan maganar mutum dai ce." |
|
5521 | 74 | 26 | سأصليه سقر |
| | | Zã Ni ƙõna shi da Saƙar. |
|
5522 | 74 | 27 | وما أدراك ما سقر |
| | | Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar! |
|
5523 | 74 | 28 | لا تبقي ولا تذر |
| | | Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari. |
|
5524 | 74 | 29 | لواحة للبشر |
| | | Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna). |
|