نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5510 | 74 | 15 | ثم يطمع أن أزيد |
| | | Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri! |
|
5511 | 74 | 16 | كلا إنه كان لآياتنا عنيدا |
| | | Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai. |
|
5512 | 74 | 17 | سأرهقه صعودا |
| | | Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa. |
|
5513 | 74 | 18 | إنه فكر وقدر |
| | | Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) |
|
5514 | 74 | 19 | فقتل كيف قدر |
| | | Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara. |
|
5515 | 74 | 20 | ثم قتل كيف قدر |
| | | Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. |
|
5516 | 74 | 21 | ثم نظر |
| | | Sa'an nan, ya yi tunãni |
|
5517 | 74 | 22 | ثم عبس وبسر |
| | | Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. |
|
5518 | 74 | 23 | ثم أدبر واستكبر |
| | | Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, |
|
5519 | 74 | 24 | فقال إن هذا إلا سحر يؤثر |
| | | Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." |
|