نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5491 | 73 | 16 | فعصى فرعون الرسول فأخذناه أخذا وبيلا |
| | | Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani. |
|
5492 | 73 | 17 | فكيف تتقون إن كفرتم يوما يجعل الولدان شيبا |
| | | To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura. |
|
5493 | 73 | 18 | السماء منفطر به كان وعده مفعولا |
| | | Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa. |
|
5494 | 73 | 19 | إن هذه تذكرة فمن شاء اتخذ إلى ربه سبيلا |
| | | Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa. |
|
5495 | 73 | 20 | إن ربك يعلم أنك تقوم أدنى من ثلثي الليل ونصفه وثلثه وطائفة من الذين معك والله يقدر الليل والنهار علم أن لن تحصوه فتاب عليكم فاقرءوا ما تيسر من القرآن علم أن سيكون منكم مرضى وآخرون يضربون في الأرض يبتغون من فضل الله وآخرون يقاتلون في سبيل الله فاقرءوا ما تيسر منه وأقيموا الصلاة وآتوا الزكاة وأقرضوا الله قرضا حسنا وما تقدموا لأنفسكم من خير تجدوه عند الله هو خيرا وأعظم أجرا واستغفروا الله إن الله غفور رحيم |
| | | Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|
5496 | 74 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يا أيها المدثر |
| | | Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi. |
|
5497 | 74 | 2 | قم فأنذر |
| | | Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi |
|
5498 | 74 | 3 | وربك فكبر |
| | | Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi, |
|
5499 | 74 | 4 | وثيابك فطهر |
| | | Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su, |
|
5500 | 74 | 5 | والرجز فاهجر |
| | | Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu. |
|