نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5471 | 72 | 24 | حتى إذا رأوا ما يوعدون فسيعلمون من أضعف ناصرا وأقل عددا |
| | | Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi. |
|
5472 | 72 | 25 | قل إن أدري أقريب ما توعدون أم يجعل له ربي أمدا |
| | | Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!" |
|
5473 | 72 | 26 | عالم الغيب فلا يظهر على غيبه أحدا |
| | | "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa." |
|
5474 | 72 | 27 | إلا من ارتضى من رسول فإنه يسلك من بين يديه ومن خلفه رصدا |
| | | "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi." |
|
5475 | 72 | 28 | ليعلم أن قد أبلغوا رسالات ربهم وأحاط بما لديهم وأحصى كل شيء عددا |
| | | "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga." |
|
5476 | 73 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يا أيها المزمل |
| | | Yã wanda ya lulluɓe! |
|
5477 | 73 | 2 | قم الليل إلا قليلا |
| | | Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan. |
|
5478 | 73 | 3 | نصفه أو انقص منه قليلا |
| | | Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi. |
|
5479 | 73 | 4 | أو زد عليه ورتل القرآن ترتيلا |
| | | Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki. |
|
5480 | 73 | 5 | إنا سنلقي عليك قولا ثقيلا |
| | | Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi. |
|