نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5460 | 72 | 13 | وأنا لما سمعنا الهدى آمنا به فمن يؤمن بربه فلا يخاف بخسا ولا رهقا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba." |
|
5461 | 72 | 14 | وأنا منا المسلمون ومنا القاسطون فمن أسلم فأولئك تحروا رشدا |
| | | "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa." |
|
5462 | 72 | 15 | وأما القاسطون فكانوا لجهنم حطبا |
| | | "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama." |
|
5463 | 72 | 16 | وأن لو استقاموا على الطريقة لأسقيناهم ماء غدقا |
| | | "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa." |
|
5464 | 72 | 17 | لنفتنهم فيه ومن يعرض عن ذكر ربه يسلكه عذابا صعدا |
| | | "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa." |
|
5465 | 72 | 18 | وأن المساجد لله فلا تدعوا مع الله أحدا |
| | | "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)." |
|
5466 | 72 | 19 | وأنه لما قام عبد الله يدعوه كادوا يكونون عليه لبدا |
| | | "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa." |
|
5467 | 72 | 20 | قل إنما أدعو ربي ولا أشرك به أحدا |
| | | Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba." |
|
5468 | 72 | 21 | قل إني لا أملك لكم ضرا ولا رشدا |
| | | Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri." |
|
5469 | 72 | 22 | قل إني لن يجيرني من الله أحد ولن أجد من دونه ملتحدا |
| | | Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi." |
|