نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5452 | 72 | 5 | وأنا ظننا أن لن تقول الإنس والجن على الله كذبا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah." |
|
5453 | 72 | 6 | وأنه كان رجال من الإنس يعوذون برجال من الجن فزادوهم رهقا |
| | | "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai." |
|
5454 | 72 | 7 | وأنهم ظنوا كما ظننتم أن لن يبعث الله أحدا |
| | | "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba." |
|
5455 | 72 | 8 | وأنا لمسنا السماء فوجدناها ملئت حرسا شديدا وشهبا |
| | | "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye." |
|
5456 | 72 | 9 | وأنا كنا نقعد منها مقاعد للسمع فمن يستمع الآن يجد له شهابا رصدا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa." |
|
5457 | 72 | 10 | وأنا لا ندري أشر أريد بمن في الأرض أم أراد بهم ربهم رشدا |
| | | "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?" |
|
5458 | 72 | 11 | وأنا منا الصالحون ومنا دون ذلك كنا طرائق قددا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam." |
|
5459 | 72 | 12 | وأنا ظننا أن لن نعجز الله في الأرض ولن نعجزه هربا |
| | | "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba." |
|
5460 | 72 | 13 | وأنا لما سمعنا الهدى آمنا به فمن يؤمن بربه فلا يخاف بخسا ولا رهقا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba." |
|
5461 | 72 | 14 | وأنا منا المسلمون ومنا القاسطون فمن أسلم فأولئك تحروا رشدا |
| | | "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa." |
|