نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5445 | 71 | 26 | وقال نوح رب لا تذر على الأرض من الكافرين ديارا |
| | | Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida." |
|
5446 | 71 | 27 | إنك إن تذرهم يضلوا عبادك ولا يلدوا إلا فاجرا كفارا |
| | | "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci" |
|
5447 | 71 | 28 | رب اغفر لي ولوالدي ولمن دخل بيتي مؤمنا وللمؤمنين والمؤمنات ولا تزد الظالمين إلا تبارا |
| | | "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka." |
|
5448 | 72 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم قل أوحي إلي أنه استمع نفر من الجن فقالوا إنا سمعنا قرآنا عجبا |
| | | Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki." |
|
5449 | 72 | 2 | يهدي إلى الرشد فآمنا به ولن نشرك بربنا أحدا |
| | | "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba." |
|
5450 | 72 | 3 | وأنه تعالى جد ربنا ما اتخذ صاحبة ولا ولدا |
| | | "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba." |
|
5451 | 72 | 4 | وأنه كان يقول سفيهنا على الله شططا |
| | | "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah." |
|
5452 | 72 | 5 | وأنا ظننا أن لن تقول الإنس والجن على الله كذبا |
| | | "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah." |
|
5453 | 72 | 6 | وأنه كان رجال من الإنس يعوذون برجال من الجن فزادوهم رهقا |
| | | "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai." |
|
5454 | 72 | 7 | وأنهم ظنوا كما ظننتم أن لن يبعث الله أحدا |
| | | "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba." |
|