نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5430 | 71 | 11 | يرسل السماء عليكم مدرارا |
| | | "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." |
|
5431 | 71 | 12 | ويمددكم بأموال وبنين ويجعل لكم جنات ويجعل لكم أنهارا |
| | | "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." |
|
5432 | 71 | 13 | ما لكم لا ترجون لله وقارا |
| | | "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah," |
|
5433 | 71 | 14 | وقد خلقكم أطوارا |
| | | "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?" |
|
5434 | 71 | 15 | ألم تروا كيف خلق الله سبع سماوات طباقا |
| | | "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?" |
|
5435 | 71 | 16 | وجعل القمر فيهن نورا وجعل الشمس سراجا |
| | | "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?" |
|
5436 | 71 | 17 | والله أنبتكم من الأرض نباتا |
| | | "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa." |
|
5437 | 71 | 18 | ثم يعيدكم فيها ويخرجكم إخراجا |
| | | "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa." |
|
5438 | 71 | 19 | والله جعل لكم الأرض بساطا |
| | | "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya." |
|
5439 | 71 | 20 | لتسلكوا منها سبلا فجاجا |
| | | "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi." |
|