نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5425 | 71 | 6 | فلم يزدهم دعائي إلا فرارا |
| | | "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." |
|
5426 | 71 | 7 | وإني كلما دعوتهم لتغفر لهم جعلوا أصابعهم في آذانهم واستغشوا ثيابهم وأصروا واستكبروا استكبارا |
| | | "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." |
|
5427 | 71 | 8 | ثم إني دعوتهم جهارا |
| | | "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." |
|
5428 | 71 | 9 | ثم إني أعلنت لهم وأسررت لهم إسرارا |
| | | "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." |
|
5429 | 71 | 10 | فقلت استغفروا ربكم إنه كان غفارا |
| | | "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." |
|
5430 | 71 | 11 | يرسل السماء عليكم مدرارا |
| | | "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." |
|
5431 | 71 | 12 | ويمددكم بأموال وبنين ويجعل لكم جنات ويجعل لكم أنهارا |
| | | "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." |
|
5432 | 71 | 13 | ما لكم لا ترجون لله وقارا |
| | | "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah," |
|
5433 | 71 | 14 | وقد خلقكم أطوارا |
| | | "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?" |
|
5434 | 71 | 15 | ألم تروا كيف خلق الله سبع سماوات طباقا |
| | | "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?" |
|