نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5422 | 71 | 3 | أن اعبدوا الله واتقوه وأطيعون |
| | | "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni." |
|
5423 | 71 | 4 | يغفر لكم من ذنوبكم ويؤخركم إلى أجل مسمى إن أجل الله إذا جاء لا يؤخر لو كنتم تعلمون |
| | | "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)." |
|
5424 | 71 | 5 | قال رب إني دعوت قومي ليلا ونهارا |
| | | Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini." |
|
5425 | 71 | 6 | فلم يزدهم دعائي إلا فرارا |
| | | "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." |
|
5426 | 71 | 7 | وإني كلما دعوتهم لتغفر لهم جعلوا أصابعهم في آذانهم واستغشوا ثيابهم وأصروا واستكبروا استكبارا |
| | | "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." |
|
5427 | 71 | 8 | ثم إني دعوتهم جهارا |
| | | "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." |
|
5428 | 71 | 9 | ثم إني أعلنت لهم وأسررت لهم إسرارا |
| | | "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." |
|
5429 | 71 | 10 | فقلت استغفروا ربكم إنه كان غفارا |
| | | "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." |
|
5430 | 71 | 11 | يرسل السماء عليكم مدرارا |
| | | "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." |
|
5431 | 71 | 12 | ويمددكم بأموال وبنين ويجعل لكم جنات ويجعل لكم أنهارا |
| | | "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." |
|