نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5412 | 70 | 37 | عن اليمين وعن الشمال عزين |
| | | Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a! |
|
5413 | 70 | 38 | أيطمع كل امرئ منهم أن يدخل جنة نعيم |
| | | Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)? |
|
5414 | 70 | 39 | كلا إنا خلقناهم مما يعلمون |
| | | A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani. |
|
5415 | 70 | 40 | فلا أقسم برب المشارق والمغارب إنا لقادرون |
| | | Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne. |
|
5416 | 70 | 41 | على أن نبدل خيرا منهم وما نحن بمسبوقين |
| | | Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba. |
|
5417 | 70 | 42 | فذرهم يخوضوا ويلعبوا حتى يلاقوا يومهم الذي يوعدون |
| | | Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita). |
|
5418 | 70 | 43 | يوم يخرجون من الأجداث سراعا كأنهم إلى نصب يوفضون |
| | | Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa. |
|
5419 | 70 | 44 | خاشعة أبصارهم ترهقهم ذلة ذلك اليوم الذي كانوا يوعدون |
| | | Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.) |
|
5420 | 71 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم إنا أرسلنا نوحا إلى قومه أن أنذر قومك من قبل أن يأتيهم عذاب أليم |
| | | Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu. |
|
5421 | 71 | 2 | قال يا قوم إني لكم نذير مبين |
| | | Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa." |
|