نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5378 | 70 | 3 | من الله ذي المعارج |
| | | Daga Allah Mai matãkala. |
|
5379 | 70 | 4 | تعرج الملائكة والروح إليه في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة |
| | | Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne. |
|
5380 | 70 | 5 | فاصبر صبرا جميلا |
| | | Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo. |
|
5381 | 70 | 6 | إنهم يرونه بعيدا |
| | | Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa. |
|
5382 | 70 | 7 | ونراه قريبا |
| | | Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa. |
|
5383 | 70 | 8 | يوم تكون السماء كالمهل |
| | | Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa. |
|
5384 | 70 | 9 | وتكون الجبال كالعهن |
| | | Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi. |
|
5385 | 70 | 10 | ولا يسأل حميم حميما |
| | | Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake. |
|
5386 | 70 | 11 | يبصرونهم يود المجرم لو يفتدي من عذاب يومئذ ببنيه |
| | | Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa, |
|
5387 | 70 | 12 | وصاحبته وأخيه |
| | | Da matarsa da ɗan'uwansa. |
|