نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5361 | 69 | 38 | فلا أقسم بما تبصرون |
| | | To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, |
|
5362 | 69 | 39 | وما لا تبصرون |
| | | Da abin da bã ku iya gani. |
|
5363 | 69 | 40 | إنه لقول رسول كريم |
| | | Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. |
|
5364 | 69 | 41 | وما هو بقول شاعر قليلا ما تؤمنون |
| | | Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. |
|
5365 | 69 | 42 | ولا بقول كاهن قليلا ما تذكرون |
| | | Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. |
|
5366 | 69 | 43 | تنزيل من رب العالمين |
| | | Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. |
|
5367 | 69 | 44 | ولو تقول علينا بعض الأقاويل |
| | | Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. |
|
5368 | 69 | 45 | لأخذنا منه باليمين |
| | | Dã Mun kãma shi da dãma. |
|
5369 | 69 | 46 | ثم لقطعنا منه الوتين |
| | | sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. |
|
5370 | 69 | 47 | فما منكم من أحد عنه حاجزين |
| | | Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. |
|