نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5323 | 68 | 52 | وما هو إلا ذكر للعالمين |
| | | Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya. |
|
5324 | 69 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الحاقة |
| | | Kiran gaskiya! |
|
5325 | 69 | 2 | ما الحاقة |
| | | Mẽne ne kiran gaskiya? |
|
5326 | 69 | 3 | وما أدراك ما الحاقة |
| | | Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? |
|
5327 | 69 | 4 | كذبت ثمود وعاد بالقارعة |
| | | Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! |
|
5328 | 69 | 5 | فأما ثمود فأهلكوا بالطاغية |
| | | To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. |
|
5329 | 69 | 6 | وأما عاد فأهلكوا بريح صرصر عاتية |
| | | Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. |
|
5330 | 69 | 7 | سخرها عليهم سبع ليال وثمانية أيام حسوما فترى القوم فيها صرعى كأنهم أعجاز نخل خاوية |
| | | (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. |
|
5331 | 69 | 8 | فهل ترى لهم من باقية |
| | | To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? |
|
5332 | 69 | 9 | وجاء فرعون ومن قبله والمؤتفكات بالخاطئة |
| | | Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. |
|