نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5277 | 68 | 6 | بأييكم المفتون |
| | | Ga wanenku haukã take. |
|
5278 | 68 | 7 | إن ربك هو أعلم بمن ضل عن سبيله وهو أعلم بالمهتدين |
| | | Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. |
|
5279 | 68 | 8 | فلا تطع المكذبين |
| | | Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa. |
|
5280 | 68 | 9 | ودوا لو تدهن فيدهنون |
| | | Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta. |
|
5281 | 68 | 10 | ولا تطع كل حلاف مهين |
| | | Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce. |
|
5282 | 68 | 11 | هماز مشاء بنميم |
| | | Mai zunɗe, mai yãwo da gulma. |
|
5283 | 68 | 12 | مناع للخير معتد أثيم |
| | | Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi. |
|
5284 | 68 | 13 | عتل بعد ذلك زنيم |
| | | Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri). |
|
5285 | 68 | 14 | أن كان ذا مال وبنين |
| | | Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya. |
|
5286 | 68 | 15 | إذا تتلى عليه آياتنا قال أساطير الأولين |
| | | Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne." |
|