نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5204 | 64 | 5 | ألم يأتكم نبأ الذين كفروا من قبل فذاقوا وبال أمرهم ولهم عذاب أليم |
| | | Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi? |
|
5205 | 64 | 6 | ذلك بأنه كانت تأتيهم رسلهم بالبينات فقالوا أبشر يهدوننا فكفروا وتولوا واستغنى الله والله غني حميد |
| | | Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde. |
|
5206 | 64 | 7 | زعم الذين كفروا أن لن يبعثوا قل بلى وربي لتبعثن ثم لتنبؤن بما عملتم وذلك على الله يسير |
| | | Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne." |
|
5207 | 64 | 8 | فآمنوا بالله ورسوله والنور الذي أنزلنا والله بما تعملون خبير |
| | | Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne. |
|
5208 | 64 | 9 | يوم يجمعكم ليوم الجمع ذلك يوم التغابن ومن يؤمن بالله ويعمل صالحا يكفر عنه سيئاته ويدخله جنات تجري من تحتها الأنهار خالدين فيها أبدا ذلك الفوز العظيم |
| | | A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma. |
|
5209 | 64 | 10 | والذين كفروا وكذبوا بآياتنا أولئك أصحاب النار خالدين فيها وبئس المصير |
| | | Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita. |
|
5210 | 64 | 11 | ما أصاب من مصيبة إلا بإذن الله ومن يؤمن بالله يهد قلبه والله بكل شيء عليم |
| | | Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne. |
|
5211 | 64 | 12 | وأطيعوا الله وأطيعوا الرسول فإن توليتم فإنما على رسولنا البلاغ المبين |
| | | Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu. |
|
5212 | 64 | 13 | الله لا إله إلا هو وعلى الله فليتوكل المؤمنون |
| | | Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara. |
|
5213 | 64 | 14 | يا أيها الذين آمنوا إن من أزواجكم وأولادكم عدوا لكم فاحذروهم وإن تعفوا وتصفحوا وتغفروا فإن الله غفور رحيم |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|