نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5172 | 61 | 9 | هو الذي أرسل رسوله بالهدى ودين الحق ليظهره على الدين كله ولو كره المشركون |
| | | Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. |
|
5173 | 61 | 10 | يا أيها الذين آمنوا هل أدلكم على تجارة تنجيكم من عذاب أليم |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi? |
|
5174 | 61 | 11 | تؤمنون بالله ورسوله وتجاهدون في سبيل الله بأموالكم وأنفسكم ذلكم خير لكم إن كنتم تعلمون |
| | | Ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani. |
|
5175 | 61 | 12 | يغفر لكم ذنوبكم ويدخلكم جنات تجري من تحتها الأنهار ومساكن طيبة في جنات عدن ذلك الفوز العظيم |
| | | Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma. |
|
5176 | 61 | 13 | وأخرى تحبونها نصر من الله وفتح قريب وبشر المؤمنين |
| | | Da wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai. |
|
5177 | 61 | 14 | يا أيها الذين آمنوا كونوا أنصار الله كما قال عيسى ابن مريم للحواريين من أنصاري إلى الله قال الحواريون نحن أنصار الله فآمنت طائفة من بني إسرائيل وكفرت طائفة فأيدنا الذين آمنوا على عدوهم فأصبحوا ظاهرين |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya. |
|
5178 | 62 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يسبح لله ما في السماوات وما في الأرض الملك القدوس العزيز الحكيم |
| | | Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
5179 | 62 | 2 | هو الذي بعث في الأميين رسولا منهم يتلو عليهم آياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة وإن كانوا من قبل لفي ضلال مبين |
| | | Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna. |
|
5180 | 62 | 3 | وآخرين منهم لما يلحقوا بهم وهو العزيز الحكيم |
| | | Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
5181 | 62 | 4 | ذلك فضل الله يؤتيه من يشاء والله ذو الفضل العظيم |
| | | Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma. |
|