نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5164 | 61 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم سبح لله ما في السماوات وما في الأرض وهو العزيز الحكيم |
| | | Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. |
|
5165 | 61 | 2 | يا أيها الذين آمنوا لم تقولون ما لا تفعلون |
| | | Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa? |
|
5166 | 61 | 3 | كبر مقتا عند الله أن تقولوا ما لا تفعلون |
| | | Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa. |
|
5167 | 61 | 4 | إن الله يحب الذين يقاتلون في سبيله صفا كأنهم بنيان مرصوص |
| | | Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna. |
|
5168 | 61 | 5 | وإذ قال موسى لقومه يا قوم لم تؤذونني وقد تعلمون أني رسول الله إليكم فلما زاغوا أزاغ الله قلوبهم والله لا يهدي القوم الفاسقين |
| | | Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Al1ah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai. |
|
5169 | 61 | 6 | وإذ قال عيسى ابن مريم يا بني إسرائيل إني رسول الله إليكم مصدقا لما بين يدي من التوراة ومبشرا برسول يأتي من بعدي اسمه أحمد فلما جاءهم بالبينات قالوا هذا سحر مبين |
| | | Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne." |
|
5170 | 61 | 7 | ومن أظلم ممن افترى على الله الكذب وهو يدعى إلى الإسلام والله لا يهدي القوم الظالمين |
| | | Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. |
|
5171 | 61 | 8 | يريدون ليطفئوا نور الله بأفواههم والله متم نوره ولو كره الكافرون |
| | | Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi. |
|
5172 | 61 | 9 | هو الذي أرسل رسوله بالهدى ودين الحق ليظهره على الدين كله ولو كره المشركون |
| | | Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. |
|
5173 | 61 | 10 | يا أيها الذين آمنوا هل أدلكم على تجارة تنجيكم من عذاب أليم |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi? |
|