نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5029 | 56 | 50 | لمجموعون إلى ميقات يوم معلوم |
| | | "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne." |
|
5030 | 56 | 51 | ثم إنكم أيها الضالون المكذبون |
| | | "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!" |
|
5031 | 56 | 52 | لآكلون من شجر من زقوم |
| | | "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)." |
|
5032 | 56 | 53 | فمالئون منها البطون |
| | | "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta." |
|
5033 | 56 | 54 | فشاربون عليه من الحميم |
| | | "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi." |
|
5034 | 56 | 55 | فشاربون شرب الهيم |
| | | "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa." |
|
5035 | 56 | 56 | هذا نزلهم يوم الدين |
| | | Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako. |
|
5036 | 56 | 57 | نحن خلقناكم فلولا تصدقون |
| | | Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba? |
|
5037 | 56 | 58 | أفرأيتم ما تمنون |
| | | Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi? |
|
5038 | 56 | 59 | أأنتم تخلقونه أم نحن الخالقون |
| | | Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? |
|