نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5017 | 56 | 38 | لأصحاب اليمين |
| | | Ga mazõwa dãma. |
|
5018 | 56 | 39 | ثلة من الأولين |
| | | Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko. |
|
5019 | 56 | 40 | وثلة من الآخرين |
| | | Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe. |
|
5020 | 56 | 41 | وأصحاب الشمال ما أصحاب الشمال |
| | | Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu? |
|
5021 | 56 | 42 | في سموم وحميم |
| | | Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi. |
|
5022 | 56 | 43 | وظل من يحموم |
| | | Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi. |
|
5023 | 56 | 44 | لا بارد ولا كريم |
| | | Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba. |
|
5024 | 56 | 45 | إنهم كانوا قبل ذلك مترفين |
| | | Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi. |
|
5025 | 56 | 46 | وكانوا يصرون على الحنث العظيم |
| | | Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma. |
|
5026 | 56 | 47 | وكانوا يقولون أئذا متنا وكنا ترابا وعظاما أإنا لمبعوثون |
| | | Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?" |
|