نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6 | 1 | 6 | اهدنا الصراط المستقيم |
| | | Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. |
|
7 | 1 | 7 | صراط الذين أنعمت عليهم غير المغضوب عليهم ولا الضالين |
| | | Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. |
|
8 | 2 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الم |
| | | A. L̃. M̃. |
|
9 | 2 | 2 | ذلك الكتاب لا ريب فيه هدى للمتقين |
| | | Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa. |
|
10 | 2 | 3 | الذين يؤمنون بالغيب ويقيمون الصلاة ومما رزقناهم ينفقون |
| | | Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa. |
|
11 | 2 | 4 | والذين يؤمنون بما أنزل إليك وما أنزل من قبلك وبالآخرة هم يوقنون |
| | | Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni. |
|
12 | 2 | 5 | أولئك على هدى من ربهم وأولئك هم المفلحون |
| | | Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara. |
|
13 | 2 | 6 | إن الذين كفروا سواء عليهم أأنذرتهم أم لم تنذرهم لا يؤمنون |
| | | Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba. |
|
14 | 2 | 7 | ختم الله على قلوبهم وعلى سمعهم وعلى أبصارهم غشاوة ولهم عذاب عظيم |
| | | Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma. |
|
15 | 2 | 8 | ومن الناس من يقول آمنا بالله وباليوم الآخر وما هم بمؤمنين |
| | | Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne. |
|