نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4939 | 55 | 38 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4940 | 55 | 39 | فيومئذ لا يسأل عن ذنبه إنس ولا جان |
| | | To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani. |
|
4941 | 55 | 40 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4942 | 55 | 41 | يعرف المجرمون بسيماهم فيؤخذ بالنواصي والأقدام |
| | | zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu. |
|
4943 | 55 | 42 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4944 | 55 | 43 | هذه جهنم التي يكذب بها المجرمون |
| | | Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita. |
|
4945 | 55 | 44 | يطوفون بينها وبين حميم آن |
| | | Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa. |
|
4946 | 55 | 45 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4947 | 55 | 46 | ولمن خاف مقام ربه جنتان |
| | | Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu. |
|
4948 | 55 | 47 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|