نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4915 | 55 | 14 | خلق الإنسان من صلصال كالفخار |
| | | Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko. |
|
4916 | 55 | 15 | وخلق الجان من مارج من نار |
| | | Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã. |
|
4917 | 55 | 16 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4918 | 55 | 17 | رب المشرقين ورب المغربين |
| | | Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã. |
|
4919 | 55 | 18 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4920 | 55 | 19 | مرج البحرين يلتقيان |
| | | Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa. |
|
4921 | 55 | 20 | بينهما برزخ لا يبغيان |
| | | A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba. |
|
4922 | 55 | 21 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|
4923 | 55 | 22 | يخرج منهما اللؤلؤ والمرجان |
| | | Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su. |
|
4924 | 55 | 23 | فبأي آلاء ربكما تكذبان |
| | | To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? |
|