نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4861 | 54 | 15 | ولقد تركناها آية فهل من مدكر |
| | | Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni |
|
4862 | 54 | 16 | فكيف كان عذابي ونذر |
| | | To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa? |
|
4863 | 54 | 17 | ولقد يسرنا القرآن للذكر فهل من مدكر |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? |
|
4864 | 54 | 18 | كذبت عاد فكيف كان عذابي ونذر |
| | | Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa? |
|
4865 | 54 | 19 | إنا أرسلنا عليهم ريحا صرصرا في يوم نحس مستمر |
| | | Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa. |
|
4866 | 54 | 20 | تنزع الناس كأنهم أعجاز نخل منقعر |
| | | Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne. |
|
4867 | 54 | 21 | فكيف كان عذابي ونذر |
| | | To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa? |
|
4868 | 54 | 22 | ولقد يسرنا القرآن للذكر فهل من مدكر |
| | | Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? |
|
4869 | 54 | 23 | كذبت ثمود بالنذر |
| | | Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin. |
|
4870 | 54 | 24 | فقالوا أبشرا منا واحدا نتبعه إنا إذا لفي ضلال وسعر |
| | | Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. |
|