نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4847 | 54 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم اقتربت الساعة وانشق القمر |
| | | Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge. |
|
4848 | 54 | 2 | وإن يروا آية يعرضوا ويقولوا سحر مستمر |
| | | Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!" |
|
4849 | 54 | 3 | وكذبوا واتبعوا أهواءهم وكل أمر مستقر |
| | | Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi. |
|
4850 | 54 | 4 | ولقد جاءهم من الأنباء ما فيه مزدجر |
| | | Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu. |
|
4851 | 54 | 5 | حكمة بالغة فما تغن النذر |
| | | Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni. |
|
4852 | 54 | 6 | فتول عنهم يوم يدع الداع إلى شيء نكر |
| | | Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama. |
|
4853 | 54 | 7 | خشعا أبصارهم يخرجون من الأجداث كأنهم جراد منتشر |
| | | ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse. |
|
4854 | 54 | 8 | مهطعين إلى الداع يقول الكافرون هذا يوم عسر |
| | | Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!" |
|
4855 | 54 | 9 | كذبت قبلهم قوم نوح فكذبوا عبدنا وقالوا مجنون وازدجر |
| | | Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi. |
|
4856 | 54 | 10 | فدعا ربه أني مغلوب فانتصر |
| | | Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako." |
|